Taliban za ta yi tattaunar zaman lafiya da Amurka
Kungiyar Taliban ta ce a shirye take ta shiga tattaunawar zaman lafiya kai-tsaye da Amurka, da nufin samar da zaman lafiya da tsaro a kasar ta Afghanistan mai fama da hare-haren ta'addanci daga kungiyoyi daban-daban.
Wallafawa ranar:
Sanarwar ta Taliban na zuwa ne yayin da ya rage kwanaki kadan a fara wani taron samar da zaman lafiya a birnin Kabul, taron da ake sa ran halartar akalla wakilan kasashen duniya 25.
Sanarwar ta ce kofa a bude ta ke ga Amurkan ta tattauna kai tsaye da ofishin da ke kula da harkokin siyasa na kungiyar wadda ta kira kan ta da ''Islamic Emirate'' don samar da zaman lafiya a kasar ta Afghanistan.
A kwanakin da suka gabata ne wata manzon musamman da ga gwamnatin Amurka mai suna Alice Wells, ta ziyarci Kabul, inda ta bayyana aniyarsu ta shiga tattaunawa da kungiyar ta Taliban.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu