Isa ga babban shafi
Syria

Kwamitin Sulhu ya amince da tsagaita wutar yakin Syria

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ya amince da kudurin neman tsagaita wuta a yakin Syria tsawon kwanaki 30, domin bai wa jami’an agaji damar gudanar da ayyukansu, da kuma kwashe marasa lafiya.

Zauren Kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya.
Zauren Kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya. REUTERS/Eduardo Munozrs
Talla

A wanna karon Rasha bata hau kujerar na ki ba kamar yadda aka zata da fari.

Jakadan Faransa a zauren majalisar dinkin duniya Francoise Delletre da ya koka bisa jinkirin daukar matakin, ya ce Faransa zata sa ido wajen ganin an aiwatar da Yarjejeniyar.

A yau Lahadi shugaban Faransa Emmanuel Macron da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel zasu gana da takwaransu na Rasha vladmir Putin dangane da batun aiwatarwa da kuma mutunta yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cinma ta tsawon kwanaki 30 a yakin kasar Syria.

Jiya Asabar aka sanar da shirin ganawar a yau, bayan da kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin duniya a amince da kudurin tsagaita wutar.

Zuwa yanzu akalla mutane 500 suka hallaka a yankin gabashin Ghouta na ‘yan tawaye, inda jiragen yakin Syria suke yi wa barin wuta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.