Turkiya ta musanta amfani da makami mai guba a Syria
Turkiya ta ce bata taba yin amfani da ko wane irin nau’in makami mai guba ba a Syria, hasalima tana daukar kwararan matakan kare fararen hula, tun bayan kaddamar da farmaki da ta yi kan mayakan Kurdawa na kungiyar YPG.
Wallafawa ranar:
Turkiya ta musanta zargin ne, bayan da wata kungiya da ke sa ido kan yakin Syria da kuma mayakan Kurdawa da ke kasar, suka zargi sojin Turkiya da kai hari da makami mai kunshe da sinadarin gas mai guba a yankin Afrin.
Mayakan kurdawan sun ce harin makami mai gubar da sojin Turkiya suka kai, ya jikkata akalla mutane shidda a jiya Juma’a.
A watan Janairu sojin Turkiya suka kaddamar da hari kan Kurdawan kungiyar YPG da ke arewacin Syria a yankin Afrin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu