Isa ga babban shafi
Maldives

Gwamnatin Maldives ta ayyana dokar ta baci

Jami’an ‘yan sandan Maldives sun cafke babban alkalin kotun kolin kasar a yayin da rikicin siyasa ke dada kamari, lamarin da ya sa shugaba Abdulla Yameen ya ayyana dokar ta baci na tsawon kwanaki 15.

An jibge jami'an tsaro a sassan Maldives bayan kafa dokar ta baci
An jibge jami'an tsaro a sassan Maldives bayan kafa dokar ta baci REUTERS
Talla

Tun hawan shugaba Yameen kan karagar mulki a shekarar 2013, lamarin kasar ya fara dagulewa bayan ya fara kama masu adawa da salon jagorancinsa.

Takaddama ta baya-bayan nan ta kunno kai ne tsakanin shugaban da Kotun kololuwa saboda shugaban ya ki bin umarnin kotu na sakin wasu ‘yan siyasa 9 da kuma maida wasu wakilan majalisa 12 kujerunsu saboda sun sauya jami'iyya.

A ranar Alhamis da ta gabata ne Kotun kololuwar ta yanke hukuncin maida wakilan majalisar kan kujerunsu, wanda ke nuna majalisar mai wakilai 85 na nan da rinjayen wakilai daga jamiyyun da ke adawa da shugaban kasar, kuma suna iya tsige shugaban ba tare da jibin goshi ba.

Ana ganin matakin na iya bada kafar maido da tsohon shugaban kasar da ke gudun hijira Mohammed Nasheed, wanda shi ne shugaban kasar mai cikakken iko na farko, amma kuma aka zarge shi da ta'addanci a shekara ta 2015.

Gwamnatin kasar cikin wata sanarwa ta ce, hukuncin kotun kolin kasar katsalandan ne cikin harkan gudanarwar Gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.