Isa ga babban shafi
Syria-Turkiyya

An kashe sojojin Turkiyya 7 a Syria

Sojojin Turkiyya biyar ne suka hallaka sa’ilin da ƴan-tawayen Ƙurdawa suka samu tankar yaƙin da sojojin ke ciki da makami.

Dakarun Turkiyya masu sintiri a yankin Hakkari.
Dakarun Turkiyya masu sintiri a yankin Hakkari. Yilmaz Kazandioglu/Reuters
Talla

A cewar hukumar soji ta Turkiyya al’amarin ya faru ne a yankin Afrin da ke arewa-maso-yammacin ƙasar Syria.

Kafar yaɗa labaru ta Anadolu ta ce hakan ya kawo yawan sojin Turkiyya da aka kashe a Syria zuwa 7 a ranar Asabar.

A watan jiya ne Turkiyya ta ƙaddamar da hare-hare kan mayakan Ƙurdawa na ƙungiyar YPG.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.