Isa ga babban shafi
Afghanistan

Mahara sun kai farmaki kan ofishin agaji a Afghanistan

Wasu mahara da suka tayar da bama-bamai sun dirar wa ofishin kungiyar agaji ta Save the Children da ke gabashin birnin Jalalabad na Afghanistan, yayin da mutane da dama suka samu rauni.

An yi amfani da mota wjen kaddamar da farmakin kan ofishin Save the Children a Jalalabad na Afghanistan
An yi amfani da mota wjen kaddamar da farmakin kan ofishin Save the Children a Jalalabad na Afghanistan REUTERS/Parwiz
Talla

Wani direban mota da ake zaton dan kunar bakin wake ne ya fara kaddamar da farmakin, yayin da maharan suka lashi takobin ci gaba da barin wuta daga kololuwar ginin ofishin.

Hotunan da aka yada sun nuna yadda mutane ke ficewa daga yankin da lamarin ya faru, kuma kawo yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin.

Yankin Jalalabad da ke kusa da kan iyakar Pakistan na yawan fama da hare-haren kungiyar Taliban, kuma har ila yau wata tunga ce na kngiyar ISIS.

Harin na baya-bayan na zuwa ne bayan wani kazamin hari da wasu ‘yan bindiga suka kai kan wani kasaitaccen otel a birnin Kabul, in da suka kashe mutane 22 da suka hada da baki daga kasashen ketare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.