Isa ga babban shafi

Syria: Turkiya ta kaddamar da farmaki kan mayakan Kurdawa

Rundunar sojin Turkiya ta kaddamar da farmaki kan mayakan Kurdawa na YPG da ke iko da yankin Afrin a arewacin kasar Syria.

Daya daga cikin tankokin yakin Turkiya yayin da suka kaddamar da farmaki kan mayakan Kurdawa na kungiyar YPG.
Daya daga cikin tankokin yakin Turkiya yayin da suka kaddamar da farmaki kan mayakan Kurdawa na kungiyar YPG. Reuters
Talla

Turkiya ta kaddamar da farmakin a jiya Juma’a ne, kwanaki kadan bayan da shugaban kasar Recep Tayyib Erdogan ya yi barazanar murkushe mayakan na YPG da ke dada samun karfin makamai a yankin na Afrin.

Sai dai farmakin ya sake bude wata sabuwar fuska, a yankin basasar kasar Syria, inda a yanzu Turkiya ke yakar mayakan Kurdawan da Amurka ke marawa baya.

Amurka ta zargi Turkiya da keta haddin iyakokin kasa da kasa, inda ta ce kamata ya yi, Turkiya ta mai da hankali wajen yakar IS ba farmaki kan kurdawa da ke Afrin ba.

A ranar Alhamis da ta gabata gwamnatin Syria, ta yi barazanar kakkabo dukkanin wani jirgin yakin Turkiya, da ya yi ganganci keta iyakar sararin samaniyarta da nufin kai ko wane irin farmaki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.