Isa ga babban shafi
Bangladesh-Myanmar

'Yan Rohingya sun gindaya sharudda kafin komawa gida

Jagororin ‘yan gudun hijirar Rohingya da ke Bangaladesh sun gindaya wasu sharudda ga hukumomi kafin su amince da yarjejeniyar fara mayar da su Myanmar cikin makon gobe. Sharuddan ka iya zamowa manyan kalubale ga shirye-shiryen hukumomin kasashen na Myanmar da Bangaladesh kan mayar da dubban ‘yan gudun Hijirar gida, aikin da za a shafe akalla shekaru biyu ana yi.

Daga cikin bukatun 'yan gudun hijirar na Rohingya, dole ne gwamnatin Myanmar ta ayyana su a matsayin cikakkun 'yan kasa baya ga hukunta wadanda suka ci zarafinsu tare da mayo musu da dukkanin muhallan da aka kwace musu a baya.
Daga cikin bukatun 'yan gudun hijirar na Rohingya, dole ne gwamnatin Myanmar ta ayyana su a matsayin cikakkun 'yan kasa baya ga hukunta wadanda suka ci zarafinsu tare da mayo musu da dukkanin muhallan da aka kwace musu a baya. 路透社。
Talla

Takaddar da jagororin dubban musulmi ‘yan gudun hijirar Rohingyar da ke sansanin na Kutupalong suka gabatar ga hukumomi sun ce baza su amince da fara komawa Myanmar ba har sai an cimma musu dukkanin bukatun da suka zayyana.

Jagororin wadanda ke wakiltar kauyuka 40 na jihar Rakhine sun ce dole ne gwamnatin Myanmar ta sanar da karbar ‘yan kabilar Rohingya a matsayin cikakkun ‘yan kasa masu ‘yancin rayuwa kamar kowa baya ga alkawarta kawo karshen kabilanci.

Haka zalika takaddar ta kuma bukaci gwamnatin Myanmar ta dawo wa ‘yan kabilar Rohingya da dukkanin gidaje makarantu asibitoci da masallatan da aka mamaye musu baya ga sake gina musu wadanda rikicin ya yi sanadiyyar lalacewarsu.

Sauran bukatun sun hadar da hukunta dukkanin Sojin Myanmar da ake zargi da kisa, cin zarafi ko ga fyade ga ‘yan kabilar ta Rohingya, bugu da kari kuma da sako dukkanin wadanda gwamnatin Myanmar ke rike da su sakamakon rikicin.

Takaddar bukatun na ‘yan gudun hijirar musulmai ‘yan kabilar ta Rohingya ta kuma nemi lallai Gwamnatin Myanmar ta daina sanya hotunan mutanen da basu jiba basu gani ba a gidajen talabijin ko dandalin sada zumunta tana ayyana su a matsayin ‘yan ta’adda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.