Isa ga babban shafi
Isra'ila

Isra'ila zata dawo da hukuncin kisa kan 'yan ta'adda

Majalisar dokokin Isra’ila na shirin kafa doka domin sauwwaka zartas da hukuncin kisa a kan wadanda mahukuntan kasar suka samu da laifin aikata ta’addanci.

Zauren Majalisar dokokin kasar Isra'ila.
Zauren Majalisar dokokin kasar Isra'ila. Reuters
Talla

Wasu ‘yan majalisa daga jam’iyyar masu ra’ayin rikau ne suka gabatar da kudurin dokar, inda tuni ya samu amincewar ‘yan majalisar 52 yayin da wasu 49 suka nuna rashin amincewarsu.

Tun shekarar 1962 ne Isra’ila ta daina zartas da hukuncin kisa kan wadanda aka samu da laifin ta’addanci, sai dai lura da cewa firaminsitan kasar Benyamin Netanyahu na goyon bayan yunkurin, manazarta da dama suna ganin cewa zai tabbata nan ba da jimawa ba.

Dawo da dokar ba ya rasa nasaba da yadda falasdinawa ke kai hare-hare da wukake akan jami’an tsaron Isra’ila musamman a cikin ‘yan shekararun baya-bayan nan.

Sai dai duk da cewa a rubuce yake karara karkashin dokokin kasar cewa, za a iya zartas da hukuncin kisa kan wadanda suka aikata kisan gilla, a zahiri ana aiwatar da hukuncin daurin rai-da-rai ne a maimakon zartas da hukuncin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.