Isa ga babban shafi
Iran

Iran: An hallaka masu zanga-zanga 10

Kafar talabijin ta kasar Iran tabbatar da cewa mutane 10, daga cikin dubban masu bore a kasar sun hallaka yayinda suke ci gaba da zanga-zangar adawa da gwamnati.

Wani sashi na birnin Teheran inda masu zanga-zanga suka fara bore.
Wani sashi na birnin Teheran inda masu zanga-zanga suka fara bore. Reuters/路透社
Talla

An samu hasarar rayukan ne bayan arrangamar da daruruwan masu zanga-zangar dauke da makamai suka yi da jami’an tsaron kasar, a lokacin da suka yi yunkurin kwace iko da wasu ofisoshin ‘yan sanda da kuma barikokin sojin kasar.

Zanga-zangar wadda aka fara a ranar Alhamis da ta gabata a garin Mashhad, ta kuma bazu zuwa sauran manyan biranen kasar, ta zama mafi girma da aka taba gani, tun bayan boren da ‘yan kasar suka yi a shekarar 2009, kan neman sauya tsarin shugabancin kasar.

Akwai fargabar cewa wannan bore zai ci gaba da gudana, idan aka yi la’akari da kiran jagororin masu zanga-zangar na cewa kada su janye daga kan aniyarsu.

Iran na daya daga cikin kasashjen duniya da ke kan gaba wajen arzikin danyen man fetur, sai dai a baya-bayannan ‘yan kasar sun fuskanci tashin farashin kayan masarufi da kuma karuwar rashin ayyukan yi da akalla kasha 28.8.

Da dama daga cikin masu zanga-zangar suna furta kalaman neman Jagoran juin juya halin Musulunci na kasar Ayatollah Ali Khamenei ya sauka daga mukaminsa.

Masu sharhi na alakanta fuskantar wannan kalubale da Iran ke yi, da yadda kasar ke kasha kudade a yakin da ta shiga a kasashen Syria da Iraqi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.