Nepal ta kafa dokar haramtawa mutane hawa tsaunin Everest
Gwamnatin Nepal ta haramtawa mutane hawa tsaunukan da ke kasar su kadai, ba tare da taimakon jami'ai ba, musamman ma tsauni mafi tsawo a duniya wato Everest.
Wallafawa ranar:
Sabuwar dokar ta kuma haramtawa guragu, da makafi yunkurin hawa tsaunin na Everest ba tare da gabatar da shaidar takarda ta tantance lafiyarsu daga asibiti ba.
Wani jami’i a ma’aikatar bunkasa yawon bude ido a kasar ta Nepal yace an kafa sabuwar dokar ce domin rage yawan hadurra da hasarar rayukan da ake samu na daruruwan mutanen da suke yin yunkurin hawa tsaunin.
A zangon karshe na shekarar 2017, akalla mutane 6 suka hallaka, ciki harda wani dan shekara 85, mai suna min Bahadur Sherchan, wanda ya yi kokarin kare kambunsa na zama mafi yawan shekaru a duniya da ya yi nasarar kai wa kololuwar tsaunin na Everest a baya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu