Isa ga babban shafi
India

Bollywood: Hukumar tace fina-finan India ta amince da 'Padmavati'

Hukumar tace fina-finan kasar India ta ce babu wata matsala a tattare da fim din Padmavati wanda masana’antar kasar ta Bollywood ta shirya shi.

Wasu daga cikin mabiya addinin Hindu a jihar Utter Pradesh da ke India, yayin da suke zanga-zangar adawa da sakin fim din Padmavati, da masana'antar Bollywood ta shirya.
Wasu daga cikin mabiya addinin Hindu a jihar Utter Pradesh da ke India, yayin da suke zanga-zangar adawa da sakin fim din Padmavati, da masana'antar Bollywood ta shirya. indianexpress
Talla

Fim din wanda ya bada labarin soyayyyar wata sarauniyar mabiya addinin Hindu da wani Sarki na Musulmi, ya haddasa jerin zanga-zanga a tsakanin mabiya addinin na Hindu a sassan kasar ta India, inda suka yi barazanar kone dukkanin gidajen Sinima a kasar da suka haska fim din, bisa dalilansu na cewa fim din tamkar cin mutunci ne a garesu.

Sai dai a hukuncinta na karshe, hukumar tace fina-finan kasar ta India ta ce babu wani abu da za’a gyara ko ragewa a tattare da labarin fim din.

A watan Nuwamba kotun kolin India, ta kori karar da wani lauya ya shigar gabanta, da ke neman kotun ta soke shirin sakin Fim din a duniya.

Padmavati ya bada labarin Sarauniyar Hindu Rajput da kuma sarkin Musulmi Alauddin Khilji, wadanda taurarin masana'antar Bollywood Deepika Padukone da Ranveer Singh suka hau kan matsayinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.