Iran-Masu zanga-zanga sun bijire wa gwamnati
Masu zanga-zanga a Iran sun bijire wa gargadin da gwamnati ta yi, inda suka ci gaba da fitowa a titunan ƙasar domin nuna fushin su kan matsi na tattalin arziƙi.
Wallafawa ranar:
Asabar ɗinnan ce rana ta 3 da ake gudanar da zanga-zangar, inda ƴan sanda suka yi arangama da mutane masu furta kalaman nuna ƙiyayya ga gwamnati a kusa da Jami’ar birnin Tehran.
A ranar Alhamis ne zanga-zangar ta fara a Mashhad, birni na biyu mafi girma a ƙasar ta Iran.
Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun rinƙa yin kalamai na nuna goyon baya ga masarautar da masu juyin-juya-halin musulunci suka kifar a shekarar 1979, yayin da wasu su sukar gwamnatin bisa mayar da hankali kan goyon bayan Falasɗinawa a maimakon bunƙasa tattalin arziƙin ƙasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu