Isa ga babban shafi
Syria

Rikicin Syria ba zai kare ba muddin Assad yana mulki - Erdogan

Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya ce yunkurin samar da zaman lafiya ta fuskar siyasa ba zai taba yiwuwa ba a Syria, muddin shugaban kasar Bashar al-Assad na karagar mulki, wanda ya bayyana a matsayin dan ta’adda.

Shugaban Turkiya Recep Tayyib Erdogan tare da takwaransa na Tunisia Beji Caïd Essebsi a lokacin da ya kai ziyara birnin Tunis. Disamba 27, 2017.
Shugaban Turkiya Recep Tayyib Erdogan tare da takwaransa na Tunisia Beji Caïd Essebsi a lokacin da ya kai ziyara birnin Tunis. Disamba 27, 2017. REUTERS/Zoubeir Souissi
Talla

Erdogan ya bayyana haka ne, yayin taron manema labarai da ya yi, bayan ganawa da shugaban Tunisia Beji Caid Essebsi.

Turkiyya dai ta jimma tana nuna adawa da shugabancin Assad tun a farkon yakin Syria, wanda a yanzu zai shiga shekara ta 7.

Turkiya na goyon bayan ‘yan adawa ne, da suka bukaci hambarar da gwamnatin Assad da kuma zargin shugaban da aikata laifukan yaki.

Kalaman Erdogan na zuwa ne kasa da kwanaki kadan bayan amincewa da gudanar da tattaunawar sulhun Syria a Rasha cikin watan Janairu, tattaunawar da itama ke fuskantar barazanar rashin yin tasiri.

A farkon wannan makon wasu kungiyoyin ‘yan tawaye 40 masu dauke da makamai suka ce ba zasu halarci tattaunawar da zata gudana a birnin Astana na kasar Kazakhstan ba, saboda rashin aminta da jagorancin kasar Rasha, wajen cimma yarjejeniyar sulhunta rikicin Syrian.

Sama da mutune dubu 400 aka kashe a Syria, bayan milyoyin da sukayi gudun hijira daga kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.