Isa ga babban shafi
Kudus

Sarki Abdallah na Jordan ya gana da Fafaroma kan Kudus

Sarki Abdallah na Jordan ya gana da Fafaroma Francis inda suka tatattauna kan matsayin Birnin Kudus da kuma matakin da Amurka ta dauka.

Fafaroma Francis a ganawarsu da Sarki Abdallah na Jordan kan birnin Kudus
Fafaroma Francis a ganawarsu da Sarki Abdallah na Jordan kan birnin Kudus REUTERS
Talla

Fadar Vatican ta ce shugabannin biyu sun tattauna ta fahimta kan tabbatar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya da makomar Birnin Kudus da kuma mutunta addinai.

Fafaroman ya bukaci ci-gaba da mutunta matsayin Birnin Kudus kamar yadda ya ke a baya, yayin da Sarki Abdallah ya yi Alla-wadai da yadda shugaba Donald Trump ya yi gaban kan sa wajen sabawa dokokin duniya.

A jiya ne dai Amurka ta yi amfani da matsayinta na mai iya hawan kujerar na-ki domin hana kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya soke matakin da shugaba Donald Trump ya dauka da ke bayyana birnin Kudus a matsayin fadar gwamnatin Isra’ila.

Sauran kasashe 14 mambobi a kwamitin sulhun ne suka amince da daftarin kudurin wanda kasar Masar ta gabatar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.