Isa ga babban shafi
Syria

Assad ya zargi Faransa da goyon bayan ta'addanci

Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Yves le Drian ya yi watsi da kalaman shugaban Syria Bashar Assad da ke zargin Faransa da taimakawa ayyukan ta’addanci, tare da cewa ba za ta iya taka rawa domin warware rikicin kasarsa ba.

Shugaban kasar Syria Bashar al-Assad
Shugaban kasar Syria Bashar al-Assad SANA/Handout via REUTERS
Talla

Yayin zantarwarsa da manema labarai a birnin Damascus, Assad ya kuma bayyana Kurdawan kasar da ke samun goyon bayan kasashe irinsu Amurka a matsayin munafukai.

Assad ya ce Munafunci matsayi ne da ya hau kan wuyan dukkanin wani wani dan kasar Syria dake yi wa wata kasa ta ketare aiki, musaman rundunar sojan Amruka.

An kiyasta cewa, Kurdawa da ke da yawan kimanin kashi 15 cikin dari na alúmmar Syria, sun hau matsayin yan ba ruwammu ne a fadan da ake gwabzawa tsakanin gwamnatin da yan tawaye. Daga bisani ne suka amfana da tabarbarewar lamura a Syrian, suka kuma samu damar shata kwarya kwaryar yancin cin gashin kan yankin nasu dake arewa maso gabashin kasar.

A nasu bangaren mayakan na Kurdawa sun mayar da martani inda suka zargi Bashar al Assad da buda kofofin kasar ga mayakan jihadin kungiyar ISIS.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.