Isa ga babban shafi
Kudus

Ƙasashen Musulmi sun bukaci wanzuwar ƙasar Falasɗinu

Shugabannin Kasashen Musulmin duniya sun bukaci mutunta gabashin Birnin Kudus a matsayin babban birnin Falasdinu da kuma bayyana Amurka a matsayin wadda ta rasa gurbin ta na mai shiga tsakani wajen sasanta rikicin Gabas ta Tsakiya.

Shugabannin kungiyar kasashen Musulmi ta Duniya
Shugabannin kungiyar kasashen Musulmi ta Duniya REUTERS/Osman Orsal
Talla

Shugabannin sun kuma yi watsi da matsayin Amurka na bayyana Birnin Kudus a matsayin babban birnin Israila.

Wadannan na daga cikin matsayin da taron shugabanin ya amince da su a kasar Turkiya.

Shugaban Turkiya Racep Tayyib Erdogan, ya buƙaci dukkanin ƙasashe masu adalci da su girmama dokokin duniya da kuma ɗaukan gabashin Ƙudus a matsayin babban birnin Falasɗinu.

Erdogan ya ƙara da cewa ƙasashen na musulunci ba za su yi ƙasa a guiwa ba wajen ganin tabbatuwar wannan buƙata ta su.

Mahalartar taron sun ce ba za ta saɓu ba, da ayyanawar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi wa Ƙudus, a matsayin babban birnin Isra’ila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.