'Matsayar Trump kan Qudus ba za ta taimaka ba'
Wasu manyan kasashen Turai sun ce matsayar da Amurka ta dauka na ayyana birnin Qudus a matsayin fadar gwamnatin Isra'ila ya saba wa matsayar majalisar dinkin duniya.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Kasashen da suka bayyana haka sun hada da Burtaniya, da France, da Jamus, da Italiya, da kuma Sweden.
A cikin wata sanarwar hadin guiwa da suka bayar ta-bakin manzanninsu a majalisar dinkin duniya, jim kadan bayan kammala taron gaggawa na kwamitin tsaron majalisar, kasashen sun ce matsayar ta Amuraka ba za ta taimaka wa yunkurin samar da zaman lafiya ba a yankin na gabas ta tsakiya.
Ko a ranar Juma'a sai da matakin na Amurka ya janyo zanga-zanga a kasashen musulmai, musamman ma a yankin gabas-ta-tsakiya.
Shi dai Trump ya tabbatar da aniyar Amurka ne na mayar da ofishin jakadancin kasar Amurka zuwa birnin Qudus, tare da ayyana birnin a matsayin fadar kasar Isra'ila.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu