Shugaban Yemen Abd Rabbo Mansour Hadi ya bai wa dakarunsa da ke samun goyon bayan kasashen duniya umurnin kaddamar sabon farmaki da nufin kwace Sanaa fadar gwamnatin kasar daga hannun ‘yan tawayen Huthi, bayan da ‘yan tawayen suka hallaka tsohon shugaban kasar Ali Abdallah Saleh a jiya Litinin. Saleh mai shekaru 75 a duniya, ya mulki kasar Yemen har na tsawon shekaru 33, in da aka tilasta ma sa sauka daga karagar mulki a 2012, in da ya kulla kawance da ‘yan tawayen na Huthi kafin daga bisani ya samu sabani da ‘yan tawayen a makon jiya. A game da wannan kisa, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr. Elharun Muhammad na Kwalejin Kimiya da Fasaha da ke garin Kaduna.
Sauran kashi-kashi
-
Yahuza Getso kan fargabar gwamnatin Najeriya na kai hari karin wasu makarantu
Yayin da ake ciki gaba da samun karuwar satar dalibai a Najeriya, Gwamnatin kasar ta bayyana fargabarta tare da yin gargadin cewa za’a iya kaiwa wasu makarantu a jihohin kasar 14 har da babban birnin tarayya Abuja.Shin hakan ya nuna gazawar gwamnatin kasa ta fannin tsaro kenan? Abdulkadir Haladu Kiyawa, ya tattauna da Dakta Yahuza Ahmad Getso masanin tsaro a Najeriyar.12/03/202403:25 -
Sheikh Sani Yahaya Jingir kan fa'idar azumin watan Ramadan
A yayin da alummar musulmi daga kasashe da dama na duniya suka fara Azumin watan Ramadan, daya daga cikin manyan malaman addninin musulunci a Nijeriya, Sheikh Muhamad Sani Yahaya Jingir, ya yi karin haske akan irin fa'idar dake tattare da Azumin watan Ramadan ga abun da yake cewa a zantawarsu da wakilinmu na Jos Tasiu zakari.11/03/202402:58 -
Saudatu Abubakar kan bikin ranar mata ta duniya
Ranar 8 ga watan Maris din kowacce shekara, rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware don bikin ranar mata da ke da aniyar lalubo matsalolin da mata ke fuskanta da kuma duba hanyoyin warware su.08/03/202403:31 -
Umar Alangawari kan kai wa motocin dakon kayan abinci da rumbuna hari
Batun kai hari tare da daka wawa kan rumbunan ajiyar kayayyakin abinci na hukumomi a wasu yankunan Najeriya na neman zama ruwan dare, la’akari da yadda a ‘yan kwanakin nan hakan ta rika faruwa, yayin da kuma a wasu lokutan aka rika tare motocin dakon abincin tare da afka musu, lamarin da ake alakantawa da tsananin tsadar rayuwa da yunwar da ke addabar dimbin mutane a Najeriya.05/03/202403:19 -
Mu'azu Magaji: Kan dambarwar Hisbah da gwamnatin Kano
Yau al’ummar Jihar Kano dake Najeriya sun tashi da labarin murabus din da shugaban hukumar Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yi daga mukamin sa, sakamakon abinda ya kira sanyaya masa gwuiwar da gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi, wajen sukar yadda suke gudanar da aikin su.01/03/202403:40