‘Yan tawayen Yemen sun kashe tsohon shugaba Saleh
‘Yan tawayen Huthi da ke iko da birnin Sanaa a kasar Yemen sun yi ikirarin kashe tsohon shugaban kasar Ali Abdullah Saleh.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Kafar yada labaran ‘yan tawayen Houthin ta tabbatar da kashe tsohon shugaban wanda a makon jiya ya bayyana matsayin sa na tattaunawa da Saudi Arabia domin kawo karshen yakin da ake tafkawa a kasar.
Wani fai-fan bidiyo na ‘yan tawayen ya nuna gawar da aka nuna cewar ta tsohon shugaban ne.
Ali Abdallah Saleh ya kwashe shekaru 30 yana jagorancin kasar kafin tilasta masa sauka a karkahsin wata yarjejeniyar da ta bai wa mataimakinsa Abedrabbo Mansour Hadi shugabanci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu