Isa ga babban shafi
Yemen

Saudiya ta amince da tayin tattaunawar sulhu kan yakin Yemen

Kasar Saudiya ta yi maraba da tayin tattaunawar sulhu da tsohon shugaban kasar Yemen Ali Abdullah Saleh ya yi mata, wanda dakarunsa ke fafatawa da rundunar hadin gwiwar da take jagoranta.

Tsohon shugaban kasar Yemen, Ali Abdullah Saleh yayin gabatar da jawabi ga wasu magoya bayansa a birnin Sanaa. 24 ga Agusta, 2017.
Tsohon shugaban kasar Yemen, Ali Abdullah Saleh yayin gabatar da jawabi ga wasu magoya bayansa a birnin Sanaa. 24 ga Agusta, 2017. Mohammed Huwais, AFP |
Talla

A jiya ne Ali Abdula Saleh, ya ce a shirye yake ya tattauna da Saudiya, muddin dakarun hadin gwiwar da ta ke jagoranta suka amince dage takunkuman hana shige da ficen kayayyakin abinci da suka dade da kakabawa ilahirin iyakokin kasar.

A baya bayannan ne fada ya kaure tsakanin dakaru masu biyayya ga Ali Abdalla Saleh da kuma mayakan Houthi masu samun goyon bayan kasar Iran, wadanda suka zarge shi da yunkurin yi wa shugabancinsu juyin mulki.

Kungiyoyin agaji sun ce har yanzu ana ci gaba da gwabza fada tsakanin mayakan na Houthi da kuma dakarun na Ali Abdalla Sale a birnin Sanaa.

Tun a shekarar 2014, mayakan Houthi suka kulla kawance da dakarun Ali Abdullah Saleh, wadanda ke yakar gwamnatin AbdRabbuh Mansur Hadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.