Isa ga babban shafi
Isra'ila

Dubban 'yan Isra'ila na zanga-zangar adawa da Netanyahu

Akalla ‘yan Isra’ila dubu 20,000 ne suka yi zanga-zanga a birnin Tel Aviv, bisa zargin da ake wa Firaministan kasar Benjamin Netanyahu, na cin hanci da Rashawa.

Dubban 'yan kasar Isra'ila yayin da suke zanga-zanga a birnin Tel Aviv.
Dubban 'yan kasar Isra'ila yayin da suke zanga-zanga a birnin Tel Aviv. REUTERS/Amir Cohen
Talla

Masu bincike na zargin Netanyahu da karbar kyautuka daga wani attajirin dan kasuwa, sai kuma zarginsa da cimma yarjejeniya da wata Jaridar kasar, wajen bai wa ayyukan gwamnatinsa fifiko, yayin da shi kuma zai taimaka mata, wajen dankwafar da abokan hamayyarta da suke aiki tare.

An dai kwashe makwanni ana gudanar da kwarya-kwaryar zanga-zangar, sai dai ta jiya Asabar ce mafi girma, musamman don nuna adawa da shirin majalisar kasar, na amincewa da wata doka da zata hana rundunar ‘yan sanda bayyana sakamakon binciken da suka yi, kan zargin na aikata ba dai dai ba da ake yi wa Netanyahu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.