An shigar da karar Hadaddiyar Daular Larabawa gaban kotun ICC
Wata Kungiyar kare hakkin dan Adam dake da cibiya a birnin London, ta bayyana shirin gurfanar da kasar Daular Larabawa a gaban kotun duniya, saboda zarginta da aikata laifukan yaki a kasar Yemen.
Wallafawa ranar:
Kungiyar mai suna Arab Organisation for Human Rights, ta zargi Daular Larabawa dake cikin kawancen kasashen dake kawance da Saudi Arabia wajen kai hari kan fararen hula.
Lauyan kungiyar Joseph Breham, yace takardun karar dake gaban kotun a Hague, sun kunshi amfani da makaman da aka haramta, da kuma daukar sojojin haya domin azabtar da mutane yayin fafata yakin.
Jami’an aikin agaji sun ce Yemen na fuskantar bala’in yunwa sakamakon yakin da tuni ya hallaka sama da mutane dubu 8,000, banda wasu mutanen 2,000 da cutar kwalara ta hallaka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu