Yara miliyan 11 ke bukatar agajin gaggawa a Yemen
Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla kananan yara miliyan 11 ke bukatar agajin gaggawa a kasar Yemen sakamakon halin kuncin da suka shiga saboda yakin da ake gwabzawa a kasar.
Wallafawa ranar:
Geert Cappalaere, Daraktan kungiyar UNICEF da ke kula da Gabas ta Tsakiya da kuma Arewacin Afirka ya ce a yau kasar Yemen ce mafi muni ga rayuwar yara kanana a duniya.
Jami’in ya ce yanzu haka yara miliyan biyu ke fama da matsanancin rashin abinci mai gina jiki, yayin da suke hasashen cewar a cikin ko wadanne minitina 10 yaro guda zai mutu daga cutar da ake iya magance ta.
A karon farko a karshen mako, jirgin Majalisar Dinkin Duniya dauke da kayan agaji ya fara sauka a Sanaa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu