Isa ga babban shafi

Amurka zata janye bai wa Kurdawan YPG makamai - Turkiya

Ministan harkokin wajen kasar Turkiya Mevlut Cavsoglu, ya ce Amurka zata daina bai wa kungiyar ‘yan tawayen Kurdawa ta YPG makamai, da ke yaki a Syria.

Wasu daga cikin mayakan Kurdawa na kungiyar YPG a birnin Qamishli da ke kasar Syria.
Wasu daga cikin mayakan Kurdawa na kungiyar YPG a birnin Qamishli da ke kasar Syria. REUTERS/Rodi Said/File Photo
Talla

Cavsoglu ya ce shugaban Amurka Donald Trump ne ya tabbatar da daukar matakin ga takwaransa na Turkiya Recep Tayyib Erdogan.

Turkiya ta dade tana adawa da goyon bayan da Amurka ke bai wa mayakan Kurdawan na YPG.

Amurka na kallon kungiyar ‘yan tawayen a matsayin wadda ke taimaka mata wajen yakar kungiyar IS a kasar Syria, yayinda ita kuma Turkiya ke daukar mayakan Kurdawan a matsayin ‘yan ta’adda, kuma reshe daga kungiyar Kurdawa da PKK da ta dade tana tada kayar baya a yankin kudu maso gabashin kasar ta Turkiya.

Har yanzu akwai sojojin Amurka akalla 2000 a kasar ta Syria, wadanda aka girke tun zamanin shugabancin Barrak Obama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.