Isa ga babban shafi
Iran

Rouhani ya yi shelar kawo karshen kungiyar IS

Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani, ya yi shelar kawo karshen kungiyar IS, nasarar da ya danganta da gudunmawar sojojin kasar da suka bada ta sadaukar da ransu, wajen fafatawa da mayakan kungiyar a kasashen Syria da Iraqi.

Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani a birnin Teheran.
Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani a birnin Teheran. ©President.ir/Handout via REUTERS
Talla

Yayin da yake gabatar da jawabi a yau Talata, Rouhani ya zargi kasar Amurka da Isra’ila bisa taimakawa mayakan na IS ta karkashin kasa.

Zalika shugaban na Iran, ya soki taron da kungiyar kasashen Larabawa suka yi ranar Lahadi da ta gabata a birnin Alkahira, wanda ya ce ko kadan ministocin kasashen, basu tattauna kan halin yunwa da rashin lafiyar da fararen hula a kasar Yemen ke fama da su ba, sakamakon yakin da kasashen suke gwabzawa da mayakan 'yan tawayen Houthi.

A nasu bangaren yayin taron gaggawan na birnin Alkahira, kasashen Larabawan sun la’anci yadda kasar Iran da kuma mayakan Hezbollah, ke haddasa fitina a yankin gabas ta tsakiya, kamar yadda suka dade suna zargi, inda suka sha alwashin kalubalantar tasirin na kasar Iran a yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.