Isa ga babban shafi

Kasashen Larabawa suna taro kan Iran

Ministocin harkokin waje na kasashen Larabawa suna gudanar da taron gaggawa a hedikwatar kungiyar kasashen Larabawan da ke birnin Alkahira.

Zauren hedikwatar kungiyar kasashen Larabawa da ke birnin Alkahira da ke kasar Masar.
Zauren hedikwatar kungiyar kasashen Larabawa da ke birnin Alkahira da ke kasar Masar. REUTERS/Asmaa Waguih
Talla

Taron na zuwa bayanda Saudi Arabia ta bukaci kasashen su tattauna kan zargin da suke yi wa kasar Iran, na haddasa fitina da barazanar tsaro a yankin gabas ta tsakiya.

A ‘yan kwanakinnan dangantaka ta sake yin tsami tsakanin, shugabancin Saudiya da gwamnatin Iran da kuma kungiyar Hezbolla.

Zalika dangantakar Saudiya ta Iran ta sake tsami, sakamakon matakin Fira ministan kasar Lebanon Sa’ad Hariri na sanar da sauka daga mukaminsa, a wata sanarwa da ya yi a birnin Riyadh.

A waccan lokacin, Sa’ad Hariri ya ce, ya dauki matakin ne sakamakon barazana ga gwamnatinsa da kuma rayuwarsa da kasar Iran da kungiyar Hezbolla ke yi, zargin da Iran ta musanta, tare da cewa Saudiya ce ta kitsa makarkashiya.

Wani batun da taron kasashen Larabawan zai tattauna a kai shi ne, yakin da ake cigaba da gwabzawa tsakanin rundunar hadaka da Saudiya ke Jagoranta da kuma mayakan Houthi, sai kuma tasirin kasar Iran a yakin Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.