Isa ga babban shafi
Lebanon

Za mu bi kadin ajiye aikin Hariri - Aoun

Shugaban kasar Lebanon Michel Aoun ya ce ya yi murna da jin cewa firaministan kasar Saad Hariri wanda ya yi murabus zai dawo gida nan ba da dadewa ba.

Murabus din Hariri ya haifar da sa-in-sa tsakanin Saudiyya da Lebanon.
Murabus din Hariri ya haifar da sa-in-sa tsakanin Saudiyya da Lebanon. FUTURE TV / AFP
Talla

Aoun ya bayyana haka ne a shafinsa na ‘Twitter’.

Ya ce ya na tsimayar dawowar Mista Hariri domin tattaunawa a kan makasudin murabus din firaministan domin samun mafita.

Mr Hariri dai ya sanar da sauka daga mukaminsa ne ta kafar talabijin daga birnin Riyadh mako daya da ya gabata, wanda hakan ya sanya ake rade-radin cewa yana karkashin daurin talala ne a kasar ta Saudiyya.

A ranan Lahadi Mr. Hariri ya sake yin wani jawabi ta wani gidan talabijin inda ya ce yana da ikon tafiya duk inda yake so, kuma zai koma gida nan ba da dadewa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.