Isa ga babban shafi
Amurka-Korea

Takaddama kan Nukiliya: Trump ya isa Korea ta Kudu

Shugaban Amurka Donald Trump ya isa birnin Seoul na kasar Korea ta Kudu domin ci gaba da ziyarar aiki ta kwanaki 11 a yankin Asiya, ziyarar da ta zo a daidai wani yanayi na zaman doya da manja tsakanin kasashen yankin sakamakon barazana daga makociyarsu Korea ta Arewa.

Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na kasar Korea ta Kudu, Moon Jae a birnin Seoul, yayinda ya isa birnin a 7 ga Nuwamba, 2017.
Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na kasar Korea ta Kudu, Moon Jae a birnin Seoul, yayinda ya isa birnin a 7 ga Nuwamba, 2017. REUTERS/Jonathan Ernst
Talla

Shirin nukiliyar Korea ta Arewa na daya daga cikin muhimman batutuwa da za su fi daukar hankalin a lokacin wannan ziyara da shugaban na Amurka ya fara yau Talata a birnin Seoul, Idan aka yi la’akari da kalaman barazana da ya furta a jiya, lokacin da yake ganawa da Firaministan Japan Shinzo Abe.

To sai dai akwai jama’a da dama, ciki harda ‘yan kasar ta Korea ta Kudu, da ke adawa da ziyarar ta mista Trump a kasar, wadanda suke ganin cewa shugaban na tafe ne sakwanni na tayar da hankula ko kuma rura wutar rikici a yankin baki daya.

Yayin da shugaba Donald Trump ke da kyakkyawar alaka da mahanga daya da Firaministan Japan Shinzo Abe dangane da irin matakan da ya kamata a dauka a kan kasar Korea ta Arewa, shi kuwa mai masaukinsa Moon Jae-In mutum ne da ake kallo a matsayin mai sassaucin ra’ayi da ke fatan sulhuntawa da makotansa.

Da farko dai an tsara cewa shugaba Trump zai kai ziyara a wani yanki da ke kan iyakar kasar Korea ta Arewa da kuma Korea ta Kudu, ziyarar da aka soke lura da halin da ake ciki na zaman dar dar tsakanin kasashen musamman daga lokacin da shugaban ya dare kan karagar mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.