Mayakan Houthi sun dauki alhakin yunkurin kai hari Riyadh
‘Yan tawayen Houthi sun dauki alhakin makami mai linzamin da aka harba da nufin rusa filin jiragen sama na birnin Riyadh da ke Saudiya, da yammacin jiya Asabar.
Wallafawa ranar:
Makami mai linzamin ya shafe akalla kilomita dari 800 kafin jami’an tsaron saudiya su kakkabo shi kasa.
Wani kakakin mayakan na Houthi, ya sha alwashin cewa zasu cigaba da kai hari cikin Saudiya da makamai masu linzami, saboda yadda sojojin kasar suka yi sanadin mutuwar fararen hula a yakin da suke fafatawa da ‘yan tawayen na Houthi a kasar Yemen.
Babu wanda ya jikkata bayan kabo makamin da jami’an tsaron Saudiya suka yi kasancewar babu mutane a wurin da ya fado.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu