Isa ga babban shafi
Saudiya

An kame 'yan gidan Sarautar Saudiya bisa zargin aikata badakala

Wata sabuwar hukumar yaki da cin hanci da rashawa na Saudiya, a karkashin Yarima mai jiran gado, Muhammad bin Salman, ta kame ‘yan gidan sarautar kasar 11, ministoci 4, da wasu tsaffin ministoci.

Yariman gidan sarautar Saudiyya Al-Waleed bin Talal a lokacin da ya kai ziyara birnin Paris.
Yariman gidan sarautar Saudiyya Al-Waleed bin Talal a lokacin da ya kai ziyara birnin Paris. REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Daga cikin wadanda aka tsare akwai Yarima Alwaleed bin Talal attajiri mai hannun jari a kamfanonin Twitter da kuma Apple.

An kame ‘yan gidan sarautar da ministocin ne bayan da hukumar ta kaddamar da bincike kan zargin aikata badakalar kudaden da aka ware, bayan aukuwar ambaliyar ruwa a jidda cikin shekarar 2009 da shawo kan barkewar kwayar cutar Mers a kasar ta Saudiya cikin Shekara ta 2012.

Sabuwar hukumar yaki da cin hancin na da karfin ikon bada umarnin kama duk wanda ake zargi da badakalar kudade, zalika tana da ikon haramta masa tafiye-tafiye.

A gefe guda kuma Sarki Salman ya sauya manyan hafsoshin rundunonin sojin kasar na kasa da ruwa.

Yayin da yake jawabi kan kamen, Ministan Shara’ar Saudiya, Shiekh Sa’ud al-Mojeb ya ce kima ko matsayin wadanda aka kama ba zai yi tasiri ba wajen yanke musu hukuncin da ya can-canta muddin aka tabbatar da zargin da ake musu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.