Isa ga babban shafi
Qatar

Qatar: 'Yan kwadago daga kasashen ketare zasu dara

Gwamnatin Qatar, a karon farko, ta fara aiwatar da sabon tsarin tafiyar da ayyukan kwadago a kasar, inda a karkashin shirin, ta fayyace mafi kankantar albashin ma’aikata da suka fito daga kasashen ketare.

Wasu daga cikin 'yan kwadagon da suka fito daga kasashen ketare, yayinda suka isa masaukinsu a birnin Doha, da ke aiki a Qatar kan shirinta na karbar bakuncin gasar kwallon kafa ta cin kofin duniya da za'a yi a shekarar 2022.
Wasu daga cikin 'yan kwadagon da suka fito daga kasashen ketare, yayinda suka isa masaukinsu a birnin Doha, da ke aiki a Qatar kan shirinta na karbar bakuncin gasar kwallon kafa ta cin kofin duniya da za'a yi a shekarar 2022. REUTERS/Stringer
Talla

Qatar ta dauki matakin ne, a dai dai lokacin da kungiyar kwadago ta duniya ke gudanar da taronta kashi na 331 a birnin Geneva, wanda aka fara ranar 26 ga oktoba, wanda kuma za’a karkare a ranar 9 ga watan Nuwamba mai zuwa.

Tun a baya kungiyar kwadagon ta ILO ta sha gargadin kasar Qatar kan yadda ta ke nuna halin ko in kula da wasu hakkokin ‘yan kwadago daga kasashen ketare da ke aiki a karkashinta.

Tun bayan fara shirin karbar bakuncin gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da za’a yi a shekara ta 2022, kungiyoyi da kasashen duniya ke caccakar Qatar dangane da zargin tauye hakkokin dubban ma’aikatan daga kasashen ketare da ke kwadago a kasar.

Qatar ta shafe tsawon lokaci tana amfani da tsarin kwadago mai tsauri da ta yi wa lakabi da “kafala” , wanda ke tilastawa ma’aikatan kwadago na kasashen ketare neman izini kamfanoni ko hukumomin da suke aiki a karkashinsu kafin sun canza aiki, ko kuma ficewa daga kasar.

Sai dai tun a watan Disambar shekara ta 2016 gwamnatin Qatar ta sanar da kawo karshen tsarin ayyukan kwadagon na “kafala”.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.