Isa ga babban shafi
Iraqi

Iraqi ta haramta tashi da saukar jirage a yankin Kurdawa

Kasar Iraqi ta bada umarni dakatar da sauka da tashin jiragen sama a birnin Erbil na yankin Kurdawa, wanda ke a matsayin martani ga zaben raba gardamar ballewa daga kasar da kurdawan suka kada.

Tashar jirgin sama a birnin Erbil na yankin Kurdawa
Tashar jirgin sama a birnin Erbil na yankin Kurdawa REUTERS/Azad Lashkari
Talla

Hukumomin Bagadaza sun ce za su ci gaba da matsin lambar tabbatar da cewa kurdawan sun mika kai

Dakatar da sufurin jiragen sama a yankin Erbil, shi ne takukumin farko da gwamnatin Bagadaza ta kakabawa kurdawan.

Dakatar da hada-hadar jiragen saman zai yi matukar tasiri a birnin da kurdawa ke gudanar da hada-hada da sauran kasashe.

Kuri’ar raba gardamar ta nuna cewa kashi sama da 90 cikin 100 na kurdawan sun amince da ballewa.

An gudanar da zaben raba gardamar duk da tsananin matsin Bagadaza, wacce ta bayyana zaben a matsayin haramtacce.

Turkiya da ita ma ke da kurdawa a cikin kasarta, ta fi nuna damuwarta tare da barazanar daukan matakan nunawa kurdawan wariya.

Daraktan filin jiragen saman Arbil, Talar Faiq Salih ya shaidawa kamfanin dilancin labaran faransa, AFP, cewa dukkanin jiragen kasar da ke shige da fice za su dakatar da jigila daga gobe Juma’a bisa hukuncin da majalisar Iraqi ta dauka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.