Isa ga babban shafi
Saudiya

Saudiya ta ba Mata ‘yancin tuka mota

Kasar Saudi Arabia a karon farko ta amince da dokar bai wa mata damar tuka mota, matakin ya kawo karshen haramcin, wanda ya nuna cewar kasar ce kasa daya tilo da ke amfani da irin wannan doka.

Mata sun samu 'yancin Tuka mota a Saudiya
Mata sun samu 'yancin Tuka mota a Saudiya REUTERS/Faisal Al Nasser/File Photo
Talla

Sarki Salman bin Abdulaziz ya bada umurnin cire haramcin daga watan Yunin shekara mai zuwa, matakin da zai ba matan damar karbar lasisi da kuma tuka mota kamar takwarorinsu na kasashen duniya.

Dokar ba matan damar tuki za ta soma aiki ne a watan Yunin 2018, domin ma mahukuntan kasar damar yin tanadin lasisin tukin ga Mata.

Kasashen duniya da kungiyoyin kare hakkin Bil Adama na kallon haramtawa mata tuki a Saudiya a matsayin wani nau’in cin zarafi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.