Isa ga babban shafi
Thailand

Hambararriyar Firaministar Thailand za ta yi shekaru 5 a gidan yari

Babbar kotun Thailand ta yankewa hambarariyar Firaministar kasar Yingluck Shinawatra hukuncin daurin shekaru 5 a gidan yari bayan samun ta da laifin rashawa. Hukuncin kotun na yau ka iya zamowa Karshen rawar da tsohuwar Firaministar ke takawa a harkokin siyasa.

Kotun ta yi zargin cewa Yingluck na da masaniya a almundahanar da aka tafka yayin bayar da kwangilar shinkafa ta sama da dala biliyan 8 amma bata dauki matakin daya kamata ba.
Kotun ta yi zargin cewa Yingluck na da masaniya a almundahanar da aka tafka yayin bayar da kwangilar shinkafa ta sama da dala biliyan 8 amma bata dauki matakin daya kamata ba. Reuters
Talla

A cewar kotun Yingluck Shinawatra ta yi sama da fadi kan wasu kudaden tallafin shinkafa da yawansu ya kai kimanin Dala biliyan 8 cikin shekarar 2014 makwanni kalilan kafin soji su yi juyin mulki.

Kotun ta ce bayan tsige ta ne kuma aka gurfanar da ita gaban kotu, ta yi ta musanta dukkanin tuhume-tuhumen da ake akanta yayinda daga bisani kuma ta gudu daga kasar zuwa hadaddiyar Daular Larabawa.

Alkalin kotun wanda ya yanke hukuncin ba tare da halartar tsohuwar Firaministar ba, ya ce Shinawatra na da masaniya kan kulalliyar da aka shirya kan kwangilar shinkafa amma ta gaza daukar matakin daya dace, duk da cewa an saba ka’idojin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.