Isa ga babban shafi
Iran

Iran za ta ci gaba da mutunta yarjejeniyar Nukiliya

Shugaban Iran Hasan Rohani, ya ce kasar shi za ta ci gaba mutunta yarjejeniyar nukiliya da ta kulla da sauran kasashen duniya a shekara ta 2015, a daidai lokacin da shugaba Donald Trump ke barazanar janye Amurka daga wannan yarjejeniya.

Shugaban kasar Iran Hassan Rohani yayin jawabin daya gabatar gaban zauren majalisar dinkin duniya, tare da jaddada matsayar kasar sa na ci gaba da mutunta yarjejeniyar Nukiliya.
Shugaban kasar Iran Hassan Rohani yayin jawabin daya gabatar gaban zauren majalisar dinkin duniya, tare da jaddada matsayar kasar sa na ci gaba da mutunta yarjejeniyar Nukiliya. Reuters
Talla

Hasan Rohani, wanda ke gabatar da jawabi a cikin zauren MDD, ya ce ya zama wajibi ga kasar ta mutunta wannan yarjejeniya, to sai dai ya yi gargadin cewa matukar Donald Trump ya yi kokarin cikas a gare ta, to Iran za ta mayar da mummunan martani.

Rohani ya ce har zuwa yau ba inda Iran ta saba wa wannan jituwa, saboda haka ba hujjar da za ta sa a zargi kasar da aikata ba daidai ba, inda ya bayyana Trump a matsayin ‘’dan daba sannan kuma bako a fagen siyasar kasa da kasa’’.

A lokacin da yake gabatar da nashi jawabi a ranar talatar da ta gabata a cikin wannan zaure, shugaban na Amurka ya bayyana Iran a matsayin kasar da ‘yan daba, ‘yan kama karya sannan maciya rashawa ke jagoranta.

Shugaba Trump ya ce nan zuwa tsakiyar watan oktoba ne zai bayyana matsayin Amurka dangane da wannan yarjejeniya wadda aka kulla kimanin shekaru biyu da suka gabata a birnin Vienna don kawo karshen shirin nukiliyar Iran.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.