Isa ga babban shafi
Myanmar

Gwamnatin Myanmar zata takaita zirga-zirgar ‘yan gudun hijirar Rohingya

Bangladesh ta ce, zata takaita zirga-zirgar ‘yan gudun hijira na kabilar Rohingya da suke shigo mata, bayan tserewa daga Myanmar.

Wasu 'yan kabilar Rohinya da ke tafiya kan hanya mai cike da tabo, bayan ketarawa kasar Bangladesh daga Myanmar.
Wasu 'yan kabilar Rohinya da ke tafiya kan hanya mai cike da tabo, bayan ketarawa kasar Bangladesh daga Myanmar. REUTERS/Danish Siddiqui
Talla

‘Yan sandan kasar sun ce tilas ne ‘yan gudun hijirar na Kabilar Rohingya, su zauna a sansanonin wucin gadin da gwamnati ta basu a maimakon fantsama cikin kasar.

Gwamnatin Bangladesh ta kuma sanar da shirinta na gina manyan sansanoni a birnin Cox’s Bazar da zasu ishi ‘yan kabilar ta Rohingya sama da 400,000 da suka tsere daga Mynamar, inda kungiyoyin kare hakkin dan’adam suka zargi sojin kasar da kone gidajen ‘yan kabilar mafi akasarinsu Musulmi, da sunan kokarin murkushe mayakan ARSA.

A karshen makonnan dangantaka ta yi tsami tsakanin kasashen biyu, bayanda Bangladesh ta zargi Mynammar ta keta mata iyaka ba bisa ka’ida ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.