Isa ga babban shafi
Korea ta Arewa

Burina shi ne mallakar makamai daidai da Amurka - Jong-un

Shugaban Korea ta Arewa Kim Jong-un, ya lashi takobin cewa sai kasarsa ta mallaki cikakken karfin makamin Nukiliya, domin daidaita kanta da Amurka, ta yadda gwamnatin Amurkan ba zata kara tunanin yi mata barazana da karfin soja ba.

Shugaban Korea ta Arewa Kim Jong-un
Shugaban Korea ta Arewa Kim Jong-un KCNA via REUTERS
Talla

Kim Jong-un ya sha alwashin ne, bayanda a jiya Juma’a Korea ta Arewan ta harba sabon makami mai linzami da ya ratsa ta sararin samaniyar kasar Japan.

Makamin dai ya kai nisan kilomita 770 zuwa sama, yayinda yayi tafiyar kilomita 3,700 ya ketara tsibirin Hokkaido na Japan kafin fadawa cikin teku.

Tuni dai taron da kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya na gaggawa, yayi alla wadai da sabon gwajin da Korea ta Arewan ta yi, kwanaki kadan bayan kakaba mata takunkumin karya tattalin arziki mafi karfi, a dalilin gwajin makamin nukiliyar da ta yi a farkon watannan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.