Isa ga babban shafi
Myanmar

Rikici ya tilastawa 'yan Rohingya 90,000 tserewa zuwa Bangladesh

Hukumomin agaji sun yi gargadin cewa Sansanonin ‘yan gudun hijira a kasar Bangladesh zai iya fuskantar tarin matsaloli saboda yawan jama’ar da ke cikinsa, tun bayan karuwar dubban Musulmi ‘yan kabilar Rohingya da ke ci gaba da tururuwa cikinsa don gujewa rikicin Myanmar.

Wasu 'yan kabilar Rohingya da suka tserewa rikici yayinda suka tafiya cikin tabo a kan iyakar Myanmar da Bangladesh, ranar 1 ga Satumban 2017.
Wasu 'yan kabilar Rohingya da suka tserewa rikici yayinda suka tafiya cikin tabo a kan iyakar Myanmar da Bangladesh, ranar 1 ga Satumban 2017. REUTERS/Mohammad Ponir Hossain
Talla

Majalisar Dinkin Duniya tace ‘yan kabilar ta Rohingya akalla dubu 90,000 ne yanzu haka suke samun mafaka a kasar Bangladesh tun bayan barkewar rikicin da aka samu a yankin su ranar 25 ga watan Agusta.

Matakin ya biyo bayan hare haren da sojojin Myanmar suka kaddamar Jihar Rakhine wanda yanzu haka yayi sanadiyar kashe daruruwan mutane.

Mafi akasarin ‘yan gudun hijirar wadanda mata da kananan yara suka fi yawa, kan yi korafin yunwa sakamakon daukar tsawon kwanaki basu ci abinci ba.

Wani daga cikin ‘yan gudun hijirar daya tsira da rayuwarsa ya shaidawa manema labarai cewa, sai da ya biya dala dari da hamsin kan kowanne daya daga cikin iyalinsa, kafin a dauko su a kwale-kwale a tsallako da su Bangaladesh.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.