Isa ga babban shafi
Korea ta Arewa

Korea ta Arewa ta yi ikirarin samun nasarar gwajin makamin nukilya

Kasar Japan ta bada tabbacin cewa Korea ta Arewa tayi gwajin makamin nukiliya kashi na shida, bayanda da kwarraru suka tabbatar da cewa motsawar kasa da karfin maki 6.3 da aka samu a wani yanki na Korea ta Arewa, ba na girgizar kasa bane, illa wanda fashewar nukiliya a karkashin kasa ya haddasa.

Shugaban kasar Korea ta Arewa Kim Jong Un yayinda ya ke duba sabon makami mai linzamin da kasar ta kera, a hoton da ba'a dauka ba, da kamfanin dillancin labaran kasar (KCNA) ya fitar a ranar 3 ga Satumban 2017.
Shugaban kasar Korea ta Arewa Kim Jong Un yayinda ya ke duba sabon makami mai linzamin da kasar ta kera, a hoton da ba'a dauka ba, da kamfanin dillancin labaran kasar (KCNA) ya fitar a ranar 3 ga Satumban 2017. Reuters
Talla

Sa’o’i kalilan da suka gabata ne, Korea ta Arewan ta sanar da cewa ta samu nasarar kera wani makamin nukiliya mai karfin gaske, da zata iya dora shi kan makami mai linzami na ICBM, domin aika shi duk inda ta so.

Sakamakon da kwararru suka fitar da safiyar yau ya nuna cewa karfin makamin Nukiliyar da Korea ta Arewan ta yi gwajinsa a dazu, ya ninka karfin makami na biyar da ta gwada a watan Satumban bara sama da sau 10.

Cikin sanawar da ta fitar, gwamnatin Korea ta Arewa, ta ce ta samu gagarumar gwajin makamin nukiliyar, wanda zata iya dora shi kan katafaren makami mai linzami na ICBM da zata iya harbawa ya isa har zuwa kasar Amurka.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.