Isa ga babban shafi
India

Magoya bayan 'Guru' sun dakatar da tarzoma

Magoya bayan malamin addibi a kasar India, Ram Rahim Singh sun janye daga arrangamar da suke cigaba da yi da jami'an tsaron kasar, wanda suka fara a ranar Juma'ar da ta gabata.

Wasu magoya bayan Guru da ke arrangama da jami'an 'yan sandan india.
Wasu magoya bayan Guru da ke arrangama da jami'an 'yan sandan india. REUTERS/Cathal McNaughton
Talla

A Halin da ake ciki jami’an tsaron kasar ta India sun kame daruruwan mutane tare da soke zirgazirgar jiragen kasa sama da 500 a arewacin kasar.

Matakin ya biyo bayan tashin hankalin da ya haddasa mutuwar mutane akalla 36, sakamakon hukuncin zaman gidan yari da wata kotun kasar ta yankewa malamin addini Ram Rahim Singh, sakamakon samunsa da laifin yiwa wasu mata biyu mabiyansa fyade.

Kakakin 'yan sandan garin Panchkula da ke jihar Haryana, Ram Niwas ya ce, zuwa yanzu akalla magoya bayan malamin da aka fi sani da Guru 800 suka damke dauke da muggan makamai.

Kimanin mutane 200 suka jikkata daga cikinsu jami’an tsaro 50, sakamakon tarzomar da magoya bayan malamin suka tada, a ranar Juma’ar da ta gabata.

Guru mai shekaru 50 yana ikirarin cewa yana da akalla mabiya miliyan 60 a sassan duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.