Isa ga babban shafi
Thailand

Kotu ta bukaci jami'an tsaro su gabatar ma ta da Shiniwatra

Kotu ta bukaci a gabatar ma ta da tsohuwar firaministar kasar Thailand Yingluck Shinawatra wadda ake zargi da aikata ba daidai ba lokacin da take rike da mukaminta.

Tsohuwar firaministar Thailand, Yingluck Shinawatra
Tsohuwar firaministar Thailand, Yingluck Shinawatra LILLIAN SUWANRUMPHA / AFP
Talla

Sojoji da ke kan karagar mulkin kasar sun tsaurara bincike musamman a binrin Bangkog, bayan da aka fara yada jita jitar cewa Shinawatra ta tsere ko kuma na kokarin tserewa daga kasar.

A wannan juma’a ne ya kamata tsohuwar firaministar ta sake bayyana a gaban kotu, to amma ba ta yi hakan ba, inda lauyoyinta ke cewa ta kasa bayyana ne saboda rashin lafiya.

Matukar dai aka sami tsohuwar firaminista Yingluck Shinawatra da laifi dangane da zargin da ake yi ma ta, to ko shakka babu za a iya yanke ma ta hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.