Isa ga babban shafi
Sa'udiyya

Sa'udiyya ta bude iyakokinta ga Mahajjatan Qatar

Sarki Salman na Sa'udiyya ya bada umarnin bude iyakar kasar da Qatar don bayar da dama ga Mahajjatan da za su shiga kasar don gudanar da ayyukan hajjinsu a bana duk da rikicin diflomasiyar da ke tsakaninsu. Tuni dai Qatar ta yi marhabun da matakin wanda ta bayyana a matsayin ci gaba da tskaninta da Sa'udiyyar la'akari da takun sakar dake tsakani.

Yarima Muhammad bin Nayef na Sa'udiyya ke gudanar da wani rangadi a wani bangare na shirye-shiryen aikin Hajjin Bana a Makka
Yarima Muhammad bin Nayef na Sa'udiyya ke gudanar da wani rangadi a wani bangare na shirye-shiryen aikin Hajjin Bana a Makka REUTERS
Talla

Sanarwa sake bude iyakokin kasar domin bai wa mahajatta damar ketarawa zuwa Sa'udiyya, shi ne sassauci irinsa na farko da Qatar ke samu tun bayan fara takun-saka da kasashen na yankin Golf 4 da suka kakaba mata takukumai bayan katse huldar diflomasiya da ita.

Sarkin Salman ya ce bayan iyakokin kasa, saudiya za kuma ta bude sararin samaniyarta ga masu amfani da jirgin sama wajen shiga kasar.

Matakin dai zuwa ne bayan wata tattaunawa tsakanain Yarima Muhammad bin Nayef na Sa'udiyyar da sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson, wanda ya dade yana kokarin shiga tsakani don yayyafa ruwa a rikicin kasashen, ko da yake dai babu cikakkken bayani kan batutuwan da suka tattauna.

Yanzu haka dai Friministan Qatar ya yi marhaba da matakin na Sa'udiyya, baya ga watsi da zarge-zargen farko da suka yi kan Sa'udiyyar na amfani da siyasa a harkokin aikin hajji da kuma haifar da barazana da alhazanta bayan furta wasu kalamai da ke nuna cewa ba za a basu kariya ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.