Iran zata takaita hukuncin kisa kan laifin safarar kwayoyi
Majalisar Kasar Iran ta amince da wata doka da zata takaita aiwatar da hukuncin kisan kai, kan mutanen da aka samu da laifin safarar miyagun kwayoyi a kasar.
Wallafawa ranar:
Ita dai sabuwar dokar ta ce mutumin da aka samu da hodar ibilis din da yawan sa ya kai kilo biyu ne zai fuskanci hukuncin kisan, sabanin yadda dokar take a yanzu.
Sabuwar dokar kuma ta ce an dage hukuncin kisa kan wanda aka samu da laifin safarar tabar wiwi daga kilo 5 zuwa kilo 50.
Kungiyar kare hakkin Bil Adama ta Amnesty International wadda ta sanya kasar Iran a matsayin kasa ta 6 a duniya da tafi aiwatar da hukuncin kisa ta yaba da sauyin.
Sabuwar dokar da ake saran kaita gaban majalisar malaman kasar da ake kira Guardian Council, zata mayar da hukuncin kisan da aka yankewa mutane 5,300 yanzu haka zuwa dauri.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu