Isa ga babban shafi
Nepal

Akwai yiwuwar karuwar wadanda suka mutu a Nepal

Mahukunta a Nepal na fargabar karuwar wadanda ambaliyar ruwa ya halaka daga mutum 66 zuwa sama baya da ake tsammanin wasu da dama sun bace a laka inda kuma ruwa ya yi awon gaba da wasu.

Da zarar damuna ta fi dubban Mutane a Indiya na zaman fargabar fuskantar ambaliyar ruwa ko kuma ruwan sama mai karfi da kan haddasa asarar rayuka da dukiyoyin al'umma kowacce shekara.
Da zarar damuna ta fi dubban Mutane a Indiya na zaman fargabar fuskantar ambaliyar ruwa ko kuma ruwan sama mai karfi da kan haddasa asarar rayuka da dukiyoyin al'umma kowacce shekara. Reuters
Talla

A cewar kungiyar bayar da agaji ta Redcross daruruwan mutane sun jikkata baya ga dubbai da suka bace yayinda gidaje da dama suka lalace, inda kuma ake fargabar samun Karin akalla mutum 56 da suka mace a nan gaba.

Yanzu haka dai jami'an agaji daga makwabtan Indiya na ci gaba da shigowa don taimakawa wajen lalubo sauran mutanen da suka bace, musamman fasinjan da ke cikin wasu motocin asafa guda biyu da suka yi batan dabo a ambaliyar ruwan.

Ambaliyar ruwan dai ta yi awon gaba da motocin da ke dauke da sama da Fasinja 50 a babbar hanya mai tazarar kilomita 200 da birnin, wadda kuma har yanzu ba a kai ga lalubo inda suke ba.

Babban Jami'in da ke kula da jihar Himalayan Sandeep Kadam ya bayyana cewa ya zuwa yanzu sun ceto gawakin mutane 17 a yankin kuma dakarun soji sun tsunduma aikin ceto don gano sauran gawakin dama tseratar da wadanda basu kai ga mutuwa ba.

Ko a watan Aprilun daya gabata ma daruruwan mutane sun halaka sanadiyyar ruwa mai karfi da tsawa da suka haddasa ambaliyar ruwa, wanda dama bisa al'ada hakan kan faru kusan kowacce shekara.

Tuni dai Firaiministan Indiya Narendra Modi ya mika sakon ta'aziyya da jimami ga iyalan wadanda lamarin ya shafa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.