Isa ga babban shafi
Israel

Isra'ila zata rufe tashar Aljazeera a fadin kasar

Isra'ila ta bayyana shirin ta na rufe tashar Aljazeera a fadin kasar saboda abinda ta kira yadda kafar yada labaran ke tinzira jama’a.

Firaministan Isra'ila Benyamin Netanyahu ya sanar da shirin rufe tashar Aljazeera
Firaministan Isra'ila Benyamin Netanyahu ya sanar da shirin rufe tashar Aljazeera REUTERS/Amir Cohen
Talla

Ministan sadarwa Ayoob Kara daga Jam’iyyar Likud ta Benjamin Netanyahu ya ce tashar Al Jazeera ta zama wata kafar farfaganda ga kungiyar mayakan ISIS da kuma tinzira rikici tsakanin matasan kasar.

Ministan ya ce kusan daukacin kasashen da ke Yankin da suka hada da Saudi Arabia da Masar da Jordan sun bayyana tashar Aljazeera a matsayin mai tada hanakali.

A ranar 27 ga watan Yuli, Firaminista Benjamin Netanyahu, ya bayyana aniyar sa na rufe tashar lokacin da aka samu arangama tsakanin Falasdinawa da jami’an tsaron Isra’ila dangane da tsauraran matakan tsaro a Masallacin Birnin Kudus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.