Isa ga babban shafi
Afghanistan

An kashe ‘Yan shi’a 29 a Masallaci a Afghanistan

Wani Harin kunar bakin wake a wani Masallachin mabiya Shia a Herat da ke kasar Afghanistan ya yi sanadiyar mutuwar Masallata 29 da kuma raunana wasu 63.

An kai harin bom masallacin 'Yan shi'a a Herat Afghanistan
An kai harin bom masallacin 'Yan shi'a a Herat Afghanistan REUTERS/Mohammad Shoib
Talla

Mai Magana da yawun ‘Yan Sandan Herat, Abdul Ahad Walizada ya ce an kai harin ne da misalin karfe 8 na dare agogon kasar lokacin da ake sallar isha.

Jami’in ya ce mutane biyu suka kai harin, daya ya tada bom kafin na biyun ya jefa gurneti.

Rahotanni sun ce ‘yan Shi’a sun fito suna gudanar da zanga-zanga a yau Laraba a Herat domin yin allawadai da mummunan harin.

Babu dai wata kungiya da ta fito ta yi ikirarin kai harin.

Amma Harin na Herat da ke kusa da iyakar Afghanistan da Iran na zuwa ne kwana guda bayan kungiyar ISIS ta dauki alhakin harin da aka kai ofishin Jakadancin Iraqi da ke birnin Kabul.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.