Isa ga babban shafi
Israel-Palestine

Quds: Akwai yiwuwar barkewar tarzoma a sallar juma'ar yau

Jami’an tsaron Isra’ila na a cikin shirin ko ta kwana dangane da yiyuwar sake barkewar tarzoma a zagayen masallacin Quds a wannan juma’a, inda tunni mahukuntan kasar suka sanar da haramta wa wadanda shekarunsu ba su kai 50 ba halartar sallar juma’a a yau.

Wani bangare na farfajiyar masallacin Quds
Wani bangare na farfajiyar masallacin Quds REUTERS/Muammar Awad
Talla

Rundunar ‘yan sandan Isra’ila ce ta sanar da daukar matakin haramtawa matasa halartar sallar ta yau biyo bayan mummunan artabun da aka yi a maracen jiya lokacin da falasdinawan ke murna dangane da janye sabbin matakan tsaro a zagayen masallacin.

Sanarwar ta ce mata da kuma wadanda shekarunsu suka haura 50 a duniya kawai ne za a bai wa damar shiga masallacin na Haram Sharif wanda yahudawan ke kira Temple Mount a yau, yayin da aka jibge wasu jami’an tsaro a kan hanyoyin da ke isar da jama’a zuwa ga masallacin da ke cikin tsohon birnin Quds.

A jiya alhamis ne Isra’ila ta sanar da janye dukkanin sabbin matakan tsaro da suka hada da cire kemarorin daukar hoto da kuma na’urorin shinshinan karafa da ta kafa a cikin masallacin, wannan kuwa sakamakon tarzomar da aka share tsawon kwanaki 13 ana gudanarwar tare da samun asarar rayuka.

Daruruwan mutane ne suka fito domin yin zanga-zangar murna dangane da wannan makati, lamarin da ya rikide zuwa tarzoma a yammacin jiya, kuma kawo yanzu rahotanni na cewa an cafke akalla falasdinawa 130 daga marecen jiya zuwa safiyar yau juma’a.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.