Isa ga babban shafi
India

Ambaliyar ruwa ta hallaka mutane 83 a India

Akalla mutane 83 ne suka rasa rayukansu, sakamakon ambaliyar ruwa da ta afkawa arewa maso gabashin kasar India, wadda kuma ta yi sanadin raba wasu mutane miliyan 2 da gidajensu.

Wasu daga cikin karkandar da ambaliyar ta shafa a India.
Wasu daga cikin karkandar da ambaliyar ta shafa a India. Reuters/ Zarir Hussain
Talla

Ambaliyar ta kuma tarwatsa dubban dabbobin da aka killace, a wani gandun dajin kasar, da ya kasance, daya daga cikin mafiya muhimmanci a duniya.

Ambaliyar wadda ta samo asali sakamakon saukar mamakon ruwan sama babu kakkautawa na tsawon makwanni 2 zuwa yanzu, ta fi shafar jihohin Assam, Arunachal Pradesh, Nagaland da kuma Manipur.

Magajin garin Assman sarbanda Sonowal ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na reuters cewa abin yafi muni a jihar, inda a nan kadai mutane 53 suka mutu a ambaliyar.

Jami’an ceto sun ce zaftarewar kasar da ta auku sakamakon ruwan samamn kamar da bakin kwarya, ita tayi sanadin rasa muhallan Mafi yawa daga cikin mutane miliyan biyun da iftila’in ya shafa.

Tuni kuma aka aike da jami’an ceto zuwa yankunan da ambaliyar ta shafa.

A gefe guda kuma ambaliyar ruwan ta mamaye gandun dajin Kaziranga da ke jihar Assam, mai dauke da karkanda akalla 2500 daga cikin 3000 da ake da su a fadin duniya, hakan yasa dabbobin suka tsere daga killacewar da akai musu, baya ga sauran dabbobin dajin, akall 63 da suka mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.