Isa ga babban shafi
Iraqi

Rundunar sojin Iraqi ta ce kiris ya rage ta murkushe IS a Mosul

Rundunar sojin kasar Iraqi, ta ce tana ta kwarin gwiwar nan da wasu sa’o’i, zata samu nasarar kwace cikakken iko da birnin Mosul daga hannun mayakan ISIS.

Wasu jami'an sojin kasar Iraqi, yayinda suke murnar samun nasara a kan mayakan ISIS a birnin Mosul.
Wasu jami'an sojin kasar Iraqi, yayinda suke murnar samun nasara a kan mayakan ISIS a birnin Mosul. Reuters
Talla

Tun a ranar 17 ga watan Oktoban shekarar da ta gabata, sojin Iraqi tare da hadin gwiwar mayakan Kurdawa na Peshmerga, wadanda jiragen yakin Amurka ke marawa baya, suka kaddamar da farmakin murkushe mayakan ISIS, da suka jima suna iko da birnin na Mosul.

Da fari a watan Janairu da ya gabata rundunar sojin Iraqi ta sanar da karbe ragamar iko da gabashin Mosul, sai dai kuma a bangaren yammacin birnin, rundunar hadin gwiwar ta fuskanci turjiya daga kungiyar ta ISIS.

A baya-bayannan dai majalisar dinkin duniya, ta yi gargadin cewa, akwai faragabar mayakan na ISIS sun yi garkuwa da akalla fararen hula dubu dari, a cikin birnin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.